Majalisar dattawa ta tsige shugaban kotun da’ar ma’aikata, Danladi Umar, bisa zarginsa da aikata ba daidai ba.
An yanke wannan hukunci ne bisa ga sashe na 157(1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (1999, da aka yi wa kwaskwarima), wanda ya baiwa majalisar dattawa ikon tsige wasu manyan jami’an gwamnati bisa bin ka’ida.
Korar ta biyo bayan zaman da majalisar tai wanda ya dauki tsawon awanni daya da rabi.
Bayan dawo da zaman majalisar, majalisar dattawa ta sanar da cewa sama da ‘yan majalisa 84 ne suka goyi bayan matakin.
Shugaban majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele ne ya dauki nauyin kudirin da ya kai ga tsige Umar, wanda ya bayyana muhimmiyar rawar da CCT ke takawa wajen kiyaye kyawawan dabi’u da rikon amana a gwamnati.