Tinubu Ya Kori Majalisar Gudanarwa Ta Jami’ar Nnamdi Azikwe, Magatakarda

Bola Tinubu sabo 720x430

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da rusa majalisar gudanarwa ta jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka a jihar Anambra tare da sauke Farfesa Bernard Ifeanyi Odoh, sabuwar mataimakin shugaban jami’ar da Misis Rosemary Ifoema Nwokike, mai rejista.

SolaceBase ta rahoto cewa Majalisar ta kasance ƙarƙashin jagorancin Ambasada Greg Ozumba Mbadiwe, ta haɗa da wasu mambobi biyar: Hafiz Oladejo, Augustine Onyedebelu, da Engr. Amioleran Osahon, da kuma Rtd. Gen. Funsho Oyenyin.
Wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai (Information & Strategy) ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, ta ce korar majalisar gudanarwar da jami’an ta ya biyo bayan rahotannin da ke cewa majalisar ta nada mataimakin shugaban kasa ba bisa ka’ida ba ba tare da bin ka’ida ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here