Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu yana cikin koshin lafiya kuma yana ci gaba da ziyarar aikinsa ta ƙasa zuwa Turkiyya kamar yadda aka tsara.
Hakan na cikin wata sanarwa a ranar Talata ta hannun mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan kafafen yaɗa labarai da sadarwa da jama’a, Sunday Dare, ya wallafa a shafinsa na X da aka tabbatar.
Bayan kammala tarbar girmamawa da aka shirya masa a Ankara, Shugaba Tinubu ya wuce tarukan haɗin gwiwa da Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan da sauran manyan jami’an gwamnati.
Tarukan na da nufin ƙarfafa alaƙar diflomasiyya tare da faɗaɗa haɗin gwiwa a muhimman fannoni daban-daban.
Daga cikin muhimman fannonin da aka mayar da hankali a kai akwai tsaro da kare ƙasa, kasuwanci da zuba jari, makamashi, da bunƙasar tattalin arziki gaba ɗaya.
Ci gaban ziyarar cikin kwanciyar hankali ya nuna ƙara ƙarfafa alaƙa tsakanin Nijeriya da Turkiyya tare da jaddada sabon yunƙurin diflomasiyya da Nijeriya ke yi a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu.
A gefe guda kuma, kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa shugaban ƙasa ya taka wani abu ne kawai a ƙasa wanda ya sa ya dan rasa daidaito na ɗan lokaci, amma babu wani abu mai tsanani da ya faru, inda ya tabbatar da cewa shugaban ƙasar yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana ci gaba da ayyukansa yadda ya kamata.
NAN













































