Ministan Sufuri Mua’zu Sambo ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta biya wani kudin fansa ba wajen ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su a harin da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna na ranar 28 ga Maris.
Cikin wata sanarwa da ministan ya fitar ga manema labarai an rawaito Sambo na cewa “ba a biya ko da sisin kobo ba na kudin fansar sako mutane 23 da aka yi garkuwa da su da sauran su.”
A cewarsa, bai kamata sojoji da hukumomin tsaro da aka dora wa alhakin ganin an sako wadannan mutanen da aka yi garkuwa da su ba, su dauki matakin da zai jefa rayuwar wadannan mutanen cikin mawuyacin hali.
Sambo daganan bayan sako wadanda lamarin ya rutsa da su, ana shirin ci gaba da gudanar da zirga-zirgar jiragen kasa batareda jinkiri ba.
“Domin dawo da ayyukan jirgin kasa, dole ne mu samar da matakan da za su tabbatar da cigaba da irin wannan lamari dan ganin hakan bai sake faruwa a kasar nan ba.
Dangane da dalilin da ya sa wadanda abin ya shafa ba su halarci taron ba, ministan ya ce suna bukatar kulawa da lafiya da kuma wasu hanyoyin da ake bukata bayan ceto su.
Daganan Ministan ya bayyana cewa bayan ganawar da shugaban kasa yayi da wadanda akayi garkuwa dasu a ranar Juma’a, tuni aka sada su da iyalansu.













































