Kimanin ma’aikatan kamfanin simintin Dangote su 27 ne wasu matasa dauke da makamai dake samun goyon bayan gwamnatin suka bindige bayan kai farmaki kamfanin domin rufe shi a ranar Laraba, tare da lalata wasu kadarorin kamfanin a masana’antar.
Manajan Daraktan Kamfanin Dangote Mista Michel Punchercos ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Legas.
Idan dai za a iya tunawa, matasan sun afkawa kamfanin simintin ne tare da wasu ‘yan banga da ke dauke da makamai domin aiwatar da kudurin majalisar dokokin jihar na kwace kamfanin simintin daga Dangote.
A ranar talata ne Majalisar ta bayar da umarnin rufe Dangote bisa zargin da kamfanin Dangote ya yi na sayen siminti na Kogi.
Sai dai izuwa yanzu dukkanin kura ta lafa ta yadda jami’an tsaro ke tsaye bisa kofofi dauke da makamai.
“Damuwar mu anan shine an harbe mutanan mu fiyeda 26 a harin ba bisa ka’ida ba.
“Muna da dukkan hotunan wadanda suka jikkata. An garzaya da wasu daga cikin wadanda aka harbe zuwa asibitin kwararru dake Lokoja,” in ji Punchercos.
Ya ce kamfanin ya dauki matakin ganin jami’an tsaro sun kamo ‘yan ta’addan, kuma za a tabbatar an dauki kwararan matakan shari’a a kansu.
“Hukumomin Dangote suna son sanar da jama’a musamman abokan huldarsu da sauran masu ruwa da tsaki game da farmakin da ‘yan banga dauke da makamai suka kai wa kamfanin simintin na Obajana, Kogi, bisa umarnin gwamnatin jihar.
Wani dan jarida da ya ziyarci asibitin ranar Juma’a ya gana da wasu daga cikin wadanda suka jikkata, wadanda suka ki cewa komai kan lamarin.
“Ku yi hakuri ba zan iya yi muku magana kan abin da ya faru saboda an ce ma na kada mu yi magana da ‘yan jaridu.
“Kamar yadda kuke gani daya daga cikin kafafu na na da bandeji saboda harbin bindiga da ya same ni a lokacin da nake cikin ofishina,” in ji wanda abin ya shafa.













































