PDP ta nada Baraka Sani, Dele Momodu da wasu a matsayin manyan daraktocin gudanarwar Kwamitin kamfe
Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP ta nada daraktoci da mataimakan daraktoci na kwamitin gudanar da yakin neman zaben jam’iyyar amatakin kasa.
Darakta-Janar na kwamitin kuma Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Tambuwal ya ce wadanda aka nada sun hada da Dele Momodu, a matsayin Daraktan Horaswa, Austin Opara, Darakta bangaren Sadarwa, Umar Bature, Daraktan Ayyuka da Abdullahi Hussaini, Daraktan mai kulada Kudi.
Sauran su ne Brig-Gen. Koko Essien, Daraktan kulada bangaren Tsaro, Hajia Baraka Sani, Darakta Kungiyar bada Tallafawa, Se Alhaji Ibrahim Bashir Darakta, gudanarwa, Kamaldeen Ajibade, Daraktan Harkokin Shari’a da Taoheed Ademola, Daraktan fasaha da sauransu.
Ya bukaci wadanda aka nada da su tuntubi babban Daraktan gudanarwa Farfesa Adewale Oladipo don karin bayani.
Tambuwal ya ce: “An yi imanin cewa sadaukarwar da kuka yi na samun nasarar yakin neman zabe zai tabbatar da amincewar da shugabannin jam’iyyarmu suka yi muku.













































