Cutar COVID-19 ta kashe ‘yan Najeriya 21 a ranar Kirsimetin wannan shekara 25 ga watan Disamba, yayin da adadin wadanda suka mutu ya zarce 3,000, a cewar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya.
NCDC ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar ta na yau da kullun da ta fitar da safiyar Lahadi.
Bayanai daga NCDC sun kuma nuna cewa adadin wadanda suka mutu sanadiyar COVID-19 a kasar ya kai 3,014.
Cibiyar ta kuma sanar da sabbin wadanda suka kamu da Covid-19 zuwa 1,305 a ranar Asabar, inda Legas ke da mutum 705.
A yanzu wadanda suka kamu a Najeriya ya kai zuwa 236,014.
NCDC ta ce, “A ranar 25 ga Disamba, 2021, an samu sabbin mutane 1305 da aka tabbatar sun kamu da cutar sannan 21 sun mutu a Najeriya.
“Kawo yanzu, an tabbatar da kamuwa da cutar guda 236, 014, an sallami 212, 357 kuma an samu mutuwar mutane 3, 014 a jihohi 36 da babban birnin tarayya.
“An samu sabbin masu kamuwa da cututtukan 1305 daga Jihohi 14 – Legas (705), Oyo (234), Ondo (88), Kaduna (79), Rivers (78), Ogun (30), Anambra (25), Kano (24) , Enugu (12), Ekiti (11), Jigawa (6), Osun (6), Plateau (6) da Zamfara (1).












































