Rikicin APC: Buhari bai goyi bayan kowane ɓangare a Kano ba

Muhammadu buhari
Muhammadu buhari

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce shi ba ya goyon bayan kowanne ɓangare a rikicin jam’iya mai mulki ta APC a Jihar Kano.

A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Shugaban Ƙasa kan yaɗa Labarai, Garba Shehu ya fitar a jiya Asabar, fadar shugaban ƙasa ta ce, “wannan ba gaskiya ba ne.

Yace “Wannan ba zai taɓa faruwa ba yayin da magana ta ke gaban kotu.
“A gaskiya Shugaba Buhari bai goyi bayan ko wanne ɓangare ba.

“Shi dai ya na goyon bayan APC a matsayin ta na jam’iya, yadda za ta zama mai ƙarfi da haɗin kai, ba wai wani ɓangare ba,” inji Garba Shehu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here