Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wata ƙungiya ta masu aikata laifi da ta dade tana kwaikwayon jami’an ’yan sanda domin damfarar jama’a a jihohin Kano, Kaduna da Katsina.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Asabar ta bayyana cewa an kama mambobin ƙungiyar ne bayan samun sahihin bayani daga jami’an leƙen asiri, inda aka cafke mutum biyar da ake zargi a ranar Alhamis, 16 ga Oktoba, 2025 da misalin ƙarfe ɗaya na rana.
Mutanen da aka kama sun haɗa da Aliyu Abbas mai shekaru 35, Sani Iliyasu mai shekaru 47, Ashiru Sule mai shekaru 41, Abubakar Yahaya mai shekaru 45, da Adamu Kalilu mai shekaru 45.
Sanarwar ta ce, dakarun tawaga ta musamman ta Special Intervention Squad ce ta kama su bayan an same su suna kwaikwayon jami’an ’yan sanda.
Rundunar ta ce an gano abubuwa da dama a hannunsu ciki har da katin bogi na aikin ’yan sanda, ankwa, kuɗin CFA 2,500, wasu takardun kuɗi na naira da suka lalace, da motar aiki kirar Peugeot 406 mai launin shuɗi mai lamba NSR-188-BD.
Bincike ya nuna cewa waɗannan mutanen sun amsa laifin yin amfani da katin bogi wajen damfarar jama’a da kuma yin wasu munanan ayyuka a jihohin Kano, Katsina da Kaduna.
Rundunar ta bayyana cewa za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike, yayin da kwamishinan ’yan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da jan kunnen masu laifi da masu kwaikwayon jami’ai.
Rundunar ta kuma shawarci jama’a su kasance masu lura, su kuma rika sanar da ofishin ’yan sanda mafi kusa idan sun ga wani motsi ko mutum da suke zargi yana da hannu a aikata laifi.












































