Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Abiodun a matsayin gwamnan jihar Ogun

Dapo Abiodun 1 650x430
Dapo Abiodun 1 650x430

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Legas a hukuncin da ta yanke na ranar Juma’a ta tabbatar da Dapo Abiodun a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan jihar Ogun na ranar 18 ga Maris din shekarar 2023.

Kotun Daukaka Karar a hukuncin mafi rinjaye da Mai Shari’a Joseph Ikyegh ya yanke, ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Ladi Adebutu, ya shigar kan zaben gwamnan jihar.

Sai dai hukuncin da mai shari’a Jane Inyang ya yanke ya amince da daukaka karar tare da umartar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta sake gudanar da sabon zabe a jihar cikin kwanaki 90.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here