
Kungiyar ‘yan bindiga ta Fano da ke yankin Amhara na ƙasar Habasha ta yi ikirarin cewa ta kwace wani babban gari bayan kazamin fada da sojojin ƙasar, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Habasha EMS da ke Amurka ta rawaito.
Mayaƙan Fano sun kai farmakin bazata kan jami’an tsaron da ke Wuchale tare da ƙwace garin, kamar yadda majiyar ta bayyana daga yankin.
Karanta wannan: Nyesom Wike ya bayyana aniyarsa ta yin hadin gwiwa da kasar Qatar
Majiyar ta ce mayaƙan na Fano sun kuma ƙwace makamai iri-iri daga hannun sojojin.
Ko da yake an ce fadan ya lafa, sojojin sun ci gaba da luguden wuta a garin tun daga tudun Ambasel, inda suka jikkata wasu fararen hula.
Mayaƙan Fano, waɗanda ke iƙirarin fafutukar kare hakkin kabilar Amhara, sun yi ta fafatawa da sojojin gwamnatin Habasha tun a watan Afrilun 2023 bayan sun bijirewa umarnin ajiye makamai.












































