Ministan Babban Birnin Tarayyar Abuja Nyesom Wike, ya bayyana aniyarsa ta yin hadakar gwiwa da kasar Qatar don bunkasa fannin yawon bude ido da inganta tsaro a babban birnin kasar.
Wike ya yi wannan tayin ne a lokacin da jakadan Qatar a Najeriya Dakta Ali Al-Hajri ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke Abuja ranar Litinin.
Ministan ya bayyana cewa Qatar na da matukar tasiri a kasashen duniya saboda karfin tattalin arziki da kuma matakin cigaba.
Karanta wannan: ECOWAS na tunanin yadda za’a sasanta da Nijar da Mali da Burkina Faso
Ya ce babban birnin tarayyar Abuja a bude take wajen yin hadin gwiwa kan harkokin yawon bude ido da kuma tsaro da za su amfanar da kasashen biyu.
A cewarsa, yawon bude ido da tsaro sune manyan abubuwan da suka sa a gaba a shirin sabunta al’amura na Shugaba Bola Tinubu.
“Zan yi farin ciki idan za mu iya samun dangantaka, musamman dangane da yawon shakatawa. Muna da dama mai yawa a nan da za mu iya bincika ta fuskar yawon shakatawa tare da Qatar, don haka zai kasance a cikin sha’awarmu idan za ku iya bincika wannan” Inji Wike.
Karanta wannan: Jami’ar Ilọrin UNILORIN ta kori dalibai 9
Ya kara da cewa, “Mu a shirye mu ke da filaye don gina cibiyar yawon buɗe ido, haka a shirye mu ke mu ga yadda za mu yi hadin gwiwa da mutanen da ke wajen Najeriya don kammala ginin hasumiyar tsaro da cibiyar al’adu ta Millennium, wadanda su ne manyan wuraren yawon bude ido a Abuja.”
Wike ya ce babban birnin tarayya Abuja ya samu nasarorin da aka samu ta fuskar tsaro da samar da ababen more rayuwa a kokarin da Shugaba Tinubu ya yi.
Karanta wannan: ‘Yan takarar Senegal sun yi kira da a kaɗa kuri’a cikin makonni 6
Ya kuma yi alkawarin bayar da himma na ci gaba da bayar da tallafi ga dukkan ma’aikatun kasashen waje a babban birnin kasar nan.
Da yake bayani, jakadan ya bayyana cewa Abuja na daya daga cikin manyan biranen Afirka da ke da damar zuba jari.
Al-Hajri ya ce Qatar a shirye ta ke ta kara huldar da ke tsakaninta da Najeriya, inda ya kara da cewa akwai damammaki na saka hannun jari a fannin yawon bude ido da ilimi da kiwon lafiya a babban birnin tarayyar Abuja.