
A ranar Talata ne gwamnatin jihar Ekiti ta tabbatar da sace dalibai da malamai da wani direba a yankin Emure-Ekiti na jihar amma ta sha alwashin ganin an ceto wadanda lamarin ya shafa.
Idan dai za’a iya tunawa wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai 6 da malaman makarantar sakandare 3 da direban motar a lokacin da suke dawowa daga Eporo-Ekiti a daren ranar Litinin.
Sai dai bayan sa’o’i da faruwar lamarin, gwamnatin jihar Ekiti a wata sanarwa da ta fitar ta yi kira ga mazauna jihar da kada su karaya domin an kara kaimi wajen ganin an ceto su.
Karanta wannan: ‘Yan sanda: Ma’aikacin Banki ya yi karyar garkuwa da kanshi a kan bashin Naira Miliyan 1.7
Sanarwar da gwamnatin jihar Ekiti ta fitar a ranar Talata ta ce: “Gwamnan jihar Ekiti Mista Biodun Oyebanji ya bukaci ‘yan jihar da kada su karaya kan sace wasu daliban makarantar da malamansu da aka yi a ranar Litinin a garin Emure-Ekiti, ya ba da tabbacin cewa ana kan kokarin ganin an ceto yaran da malamansu.”
An bayyana Gwamna Biodun Oyebanji yana bayyana garkuwar a matsayin rashin kyautawa, kuma ba za’a amince da shi ba, yana mai cewa babu abin da zai rage a kokarin kubutar da su.
Karanta wannan: Kasashen Mali da Burkina Faso sun mikawa ECOWAS wasikar ficewa a hukumance
Gwamnatin Ekiti ta ce “Hukumomin tsaro a jihar tuni sun fara bin diddigin wadanda suka sace daliban tare da ba da umarnin a dawo da daliban da malamansu lafiya.
“Gwamna Oyebanji ya ce ana kara daukar matakan tsaro a fadin jihar da nufin fatattakar ‘yan ta’adda daga maboyarsu,” in ji sanarwar.
Yayin da yake kira ga ‘yan jihar da su kara kwantar da hankula da kuma lura, har ya bukace su da su ba jami’an tsaro hadin kai, ta hanyar samar da bayanan da suka dace ga hukuma.












































