NAHCON ta samu rangwamen Naira biliyan 19 don aikin Hajjin 2026

NAHCON Chairman Prof Abdullahi Saleh Usman sabo 750x430

Shugaban hukumar kula da Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana cewa hukumar ta samu rangwamen kuɗi na Naira biliyan 19 ga masu niyyar zuwa aikin Hajji na shekarar 2026.

Farfesa Usman ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Kano, yayin da yake ganawa da manema labarai kan sakamakon ziyarar aikin da ya kai kwanan nan zuwa ƙasar Saudiyya.

Ya ce an samu wannan rangwame ne bayan tattaunawa da masu bayar da hidima a Saudiyya tare da kwamitocin jin daɗin alhazai na jihohi a Najeriya.

A cewarsa, yarjejeniyar ta kai ga adana fiye da Naira 200,000 ga kowane ɗan Najeriya da zai halarci aikin Hajji, inda aka bai wa Najeriya kujeru 66,910 na shekarar 2026.

Ya kara da cewa a lokacin ziyarar, NAHCON ta sanya hannu kan kwangilolin hidima da kamfanin Mashariq Dhahabiyya domin gudanar da ayyukan Masha’ir, da kuma Daleel Al-Ma’aleem domin sufuri.

Haka kuma an samu ingantaccen masauki da abinci a yankin Markaziyya na Madina a farashi mai sauki.

Hukumar ta kuma bayyana cewa kuɗin aikin Hajji na 2026 za su kasance kamar haka: Maiduguri/Yola – Naira miliyan 8.12, sauran jihohin Arewa – Naira miliyan 8.24, sannan jihohin Kudu – Naira miliyan 8.56.

Karanta: Hukumar jin daɗin  Alhazai a Kano ta sanya wa’adin rufe biyan kashi 50 cikin 100 na kujerun Hajjin 2026

An umurci kwamitocin jin daɗin alhazai na jihohi da su tura kashi 50 cikin 100 na kuɗin zuwa hukumar kafin 8 ga Oktoba, 2025, sannan a kammala cikakken biyan kuɗin daga masu niyyar tafiya kafin 31 ga Disambar 2025.

Farfesa Sale ya bayyana cewa sanya wa’adin biyan kuɗi ya zama dole domin samun damar yin tanadi tun da wuri da kuma gudanar da shirye-shirye cikin tsari.

Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da gudanar da aikin Hajji na 2026 cikin kwanciyar hankali.

Ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su ba da goyon baya ga hukumar, domin a cimma nasarar da ake buri wajen gudanar da aikin Hajji mai tsafta da nasara.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here