Sauye-sauyen CBN za su daidaita tattalin arziki, da dawo da amincewar masu zuba hannun jari – Cardoso

IMG 20251003 WA0045 768x576 1 750x430

Gwamnan Babban Bankin ƙasa (CBN), Mista Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa sauye-sauyen da bankin ya aiwatar suna da nufin daidaita tattalin arzikin ƙasa, dawo da amincewar masu zuba jari, tare da rage hauhawar farashi zuwa ƙasa da kashi goma cikin ɗari a matsakaicin lokaci.

Cardoso ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Lagos, yayin tattaunawa da aka yi da shi a wajen bude jerin laccocinsa na farko a makarantar koyar da harkokin kasuwanci ta Lagos (LBS), mai taken “Samar da Jagoranci a nan gaba tare da inganta manufofin Kuɗi da kuma gina ƙasa” wadda Laccar ta samu halartar ɗaliban jami’o’i, masana harkokin kudi, da kwararrun masana’antu.

A jawabinsa, ya ce ƙalubale da dama sun kasance wajen daidaita tattalin arzikin ƙasa, amma gaskiya da aiki tukuru sun taimaka wa CBN wajen komar da tattalin arziki zuwa hanyar bunƙasa.

Ya bayyana cewa sauye-sauyen da aka gudanar cikin shekaru biyu da suka gabata sun taimaka wajen dawo da gaskiya da amincewar masu zuba jari, ciki har da amfani da katin cire kuɗin Naira a ƙasashen waje da kuma biyan bashi na dala biliyan bakwai da aka gada.

Ya kara da cewa a lokacin da ya hau kujerar gwamna a 2023, tattalin arzikin Najeriya na fama da hauhawar farashi, raguwar ajiya ta waje, ƙarancin amincewar masu zuba jari da matsaloli a kusan dukkanin ma’aunin tattalin arziki.

Ya ce bankin ya ɗaga farashin ruwa sama da maki 800 don yaƙar hauhawar farashi, ya ƙarfafa kula da kudaden shiga, tare da kara adadin ajiya zuwa sama da dala biliyan 42.

Cardoso ya bayyana cewa yawan jama’ar da ke samun damar amfani da tsarin banki ya ƙaru daga kashi 56 cikin ɗari a 2020 zuwa sama da kashi 64 cikin ɗari a 2025, bayan faɗaɗa bankunan tafi-da-gidanka da na wayar salula.

Labari mai alaƙa: CBN ya yi alkawarin samar da sababbi kuma wadatattun takardun Naira

Haka kuma ya ce hauhawar farashi da ya kai kusan kashi 35 cikin ɗari, yanzu ya sauka zuwa kashi 20, tare da GDP na ƙasa ya karu da kashi 4.2 cikin ɗari a zangon biyu na shekarar 2025.

Ya kuma jaddada cewa sahihanci da gaskiya su ne zuciyar kowace cibiyar kudi, inda ya nuna muhimmancin bin alkawura don samun amincewar jama’a da masu zuba jari.

Ya bayyana cewa a ƙarƙashin jagorancinsa, CBN ya fara buga bayanan kudi na shekara-shekara bayan an dakatar da hakan na tsawon shekaru.

A jawabin maraba, Shugabar Makarantar koyar da harkokin Kasuwanci ta Lagos, Farfesa Olayinka David-West, ta yaba da wannan shiri na CBN, tana mai cewa zai ƙarfafa tattaunawa tsakanin masana harkokin tattalin arziki da al’umma.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here