Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a ranar Lahadi ya shiga tsakani a rikicin siyasar da ya barke tsakanin Hon. Kabiru Alhassan Rurum da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, wanda ya kai ga sulhunta ‘yan siyasar biyu.
An cimma sulhun ne biyo bayan taron da gwamnan ya kira domin warware sabani tsakanin fitattun ‘yan siyasa daga yankin kudancin jihar.
Da yake jawabi bayan taron, Hon. Rurum, wanda ke wakiltar kananan hukumomin Rano/Bunkure/Kibiya a Majalisar Wakilai, ya tabbatar da cewa shugabannin biyu sun warware sabanin da ke tsakaninsu kuma sun sake hadewa.
Ya ce sun yarda su yi wa juna afuwa tare da yin aiki tare domin ci gaban magoya bayansu da jam’iyya.
Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwar da Babban Sakataren Yada Labaran GwamnanMustapha Muhammad, ya fitar a ranar Lahadi.
Rurum ya kuma yaba wa Gwamna Yusuf kan rawar da ya taka wajen dawo da zaman lafiya, inda ya bayyana shiga tsakanin da gwamnan yayi a matsayin wani mataki da ya zo daidai da lokaci kuma mai muhimmanci.
Sanata Kawu Sumaila, wanda ke wakiltar Mazabar Kano ta Kudu, a majalisar Dattawa, ya bayyana sabanin da ya faru a matsayin rashin fahimta tare da danganta shi da “aikin Shaidan.”
Har ila yau, Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su watsar da rikicin da suka yi a baya tare da mai da hankali kan karfafa jam’iyyar gabanin zaben gama gari.
Taron sulhun ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, Alhaji Muhammad Jamu, Shugaban APC Umar Haruna Doguwa, Sanata Kawu Sumaila, da Hon. Kabiru Alhassan Rurum.
‘Yan siyasar biyu sun kuma gayyaci magoya bayansu zuwa taron tabbatar da Sanata Kawu Sumaila a matsayin dan takarar Sanatan Kano ta Kudu wanda aka shirya gudanarwa a ranar Litinin, 18 ga Mayun 2026.












































