Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulinci a Najeriya (NSCIA), Sa’ad Abubakar III, ya ayyana Litinin, 18 ga Mayun 2026, a matsayin ranar daya ga watan Dhul Hijjan shekarar 1447 bayan Hijira (AH), biyo bayan ganin jinjirin wata.
Shugaban Kwamitin Shawarwari kan Harkokin Addini na Majalisar Sarkin Musulmi ta Sokoto kuma Wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewar sanarwar, ganin watan yana nuni da fara watan Dhul Hijjah, wata na 12 kuma na karshe a kalandar Musulunci ta wata, wanda ake dauka a matsayin daya daga cikin mafi tsarki a Musulunci.
Majalisar Sarkin Musulmi ta bayyana cewa wannan wata mai alfarma yana da matukar muhimmanci ga Musulmai a duniya baki daya domin ya zo daidai da gudanar da aikin Hajji na shekara da kuma bikin Idin Babbar Sallah.
“Da wannan sanarwa, Musulmai a Najeriya da ma wajen Najeriya za su fara shirye-shiryen ibada da bukukuwan da ke da alaka da Zulhijja, ciki har da bikin Idin Babbar Sallah, wanda ake sa ran zai zo ranar Laraba, 27 ga Mayu, 2026 (10 ga Dhul Hijja), idan ba a samu canji ba,” in ji sanarwar.
Majalisar ta yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci mai tsarki wajen addu’a, tunani da sabunta ibada, tare da addu’ar samun zaman lafiya, hadin kai da ci gaba a Najeriya.
Ta kuma ba da shawara ga jama’a da su dogara ne kawai kan sanarwa ta hukuma daga Majalisar Sarkin Musulmi da sauran manyan hukumomin Musulunci wajen samun sabuntawa game da gudanar da ibadar wannan kakar.












































