Yanzu-Yanzu: Kotu ta bada belin Nasir El-Rufai kan miliyan 100

Nasir El Rufai

Alkalin Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, a ranar Litinin ta bada belin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai kan kudi Naira miliyan 100, tare da wanda zai tsaya masa da zai bayar da irin wannan kudi.

Da take yanke hukunci, Mai Shari’a Abdulmalik ta sanya wasu tsauraran sharudda da wanda ake tuhuma dole ya cika kafin ya kammala sharudan belin.

Kotu ta ce wanda zai tsaya masa dole ya zauna a yankin Maitama ko Asokoro na Abuja, sannan ya mika ainihin Takardar Shaidar Mallaka ta wani fili a sashen rajistar kotu.

Haka kuma, wanda zai tsaya masa dole ya kasance ma’aikacin gwamnatin tarayya wanda bai yi kasa da Matakin Aiki 17, sannan ya gabatar da shaidar karbar albashi na akalla watanni uku, wadda manajan banki shi zai rubuta takardar cikin ikon kotu.

Kotun ta kara umartar cewa wanda zai tsaya masa ya gavatar takardar sheda ta rantsuwa kan ya amince da komai, ya kuma shiga yarjejeniyar belin, sannan ya mika sabon hoton fasfo ga sashen rajistar kotu.

A matsayin wani bangare na sharuddan belin, El-Rufai dole ya mika duk ingantattun fasfo dinsa na kasashen waje ga sashen rajistar kotu.

Kotu ta kuma umarci a mika wasiƙar tabbatarwa daga sashen da wanda zai tsaya masa yake aiki, tare da takardar shaidar biyan haraji ta watanni shida da suka gabata.

Alkali Abdulmalik ta kara umartar wanda ake tuhuma da ya kai rahoto a hedikwatar Hukumar Tsaro ta DSS kowace Juma’a ta karshen wata da karfe 10 na safe domin ya sanya hannu a littafin halarta har sai an yanke hukunci kan shari’ar.

Alkaliyar ta gargadu cewa rashin bin sharudan zai kai ga soke belin kai tsaye.

Bugu da kari, kotun ta umarci wanda ake tuhuma da ya mika wasikar shaida daga Shugaban Majalisar Masarautar Kaduna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here