Majalisar wakilai ta bukaci a gudanar da bincike kai tsaye, cikakke kuma mai zaman kansa kan zargin kashe wasu masu zanga-zangar lumana da jami’an soja suka yi a jihar Adamawa.
Wannan bukata ta biyo bayan amincewa da wata muhimmiyar shawarar gaggawa da dan majalisa Kwamoti Laori na PDP daga Adamawa ya gabatar a zaman majalisar, inda ya nuna damuwa kan rikice-rikicen da ke ci gaba da faruwa a ƙaramar hukumar Lamurde tare da bukatar gano duk jami’an tsaro da suka aikata laifi a hukunta su.
Sanarwar ta nuna cewa rikicin da ya barke a yankin ya janyo rasa rayuka, lalacewar dukiya da haifar da tashin hankali tsakanin al’ummomi da ke fama da matsalar tsaro tun da dadewa, musamman a wani lokaci da ƙasa ke fama da ta’addanci, satar mutane da barna daga kungiyoyin da ke addabar al’umma.
Ya bayyana cewa rikicin Lamurde bai kamata ya zamo wani abu da zai ƙara yaduwa ba, musamman ganin cewa rahoton ya yi nuni da kisan mata marasa makamai guda takwas ciki har da yarinya mai shekaru 13 tare da jikkatar wasu fiye da talatin da ke jinya a asibitocin Numan da Yola, lamarin da aka danganta shi da irin abin da ya faru a garuruwan Dong, Kodomti, Lawaru, Nzuruwe da Shaforon a shekarar 2017.
Karanta: Gwamnan Bauchi ya karyata jita-jitar sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP
Majalisar ta bayyana wannan lamari a matsayin mummunar karya dokokin kare hakkin dan adam, kuma abin da ba zai taɓa kasancewa da hujja ba, tare da bukatar gaggauta inganta sahihiyar hulɗa da al’umma domin dawo da amincewa ga hukumomin tsaro.
A zaman da aka yi, shugaban majalisar Abbas Tajudeen ya umurci kwamitocin majalisa kan kare hakkin bil’adama, tsaro, da harkokin cikin gida su kai ziyarar gano gaskiya zuwa Lamurde a cikin makonni biyu domin mika rahoto kan matakan da majalisar za ta dauka.
Majalisar ta bukaci babban hafsan tsaro ya umurci dukkan jami’an soja da aka tura Lamurde da sauran sassan Adamawa da su yi hakuri, su aiwatar da aikinsu bisa ƙa’ida kuma tare da cikakken ƙwarewa.
Sannan ta umurci kwamitin bin diddigin oda da ya tabbatar da bin umarnin majalisar tare da yin addu’a jim kadan domin wadanda suka rasu.
NAN













































