Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya karyata rahoton da ya yi zargin cewa ya fita daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar PRP, inda ya bayyana wannan jita-jita a matsayin rahoto marar tushe da yaudara.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Mukhtar Gidado ya fitar a Bauchi, gwamnatin jihar ta bayyana cewa gwamnan bai taɓa tunanin sauya sheƙa daga PDP ba kuma bai yi wani yunƙuri na komawa wata jam’iyya ko kusantar PRP ba.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan jita-jita ta samo asali ne daga tunanin marubucin da ya ƙirƙiro labarin, wanda gwamnati ta ce ba shi da wani tushe kuma wata magana ce da za a yi watsi da ita saboda rashin ma’ana da neman daukaka.
Karanta: A gaggauce: Gwamna Fubara ya fice daga PDP zuwa APC
Gwamnatin ta bayyana cewa shiru a irin wannan lokaci na iya zama kamar amincewa da ƙarya, don haka wajibi ne a fayyace cewa gwamnan na da cikakken ‘yancin da kundin tsarin mulki ya ba shi na danganta kansa da duk wata hanya ta siyasa da ya ga ta dace domin ci gaban kasa da zaman lafiya.
Sanarwar ta ce ko da lokaci ya kai ga yanke shawara a nan gaba, wannan hukuncin ba zai fito daga masu yada jita-jita marasa gaskiya ba, kuma ba zai kasance sakamakon tasirin mutanen da ke neman amfani da fitintinu wajen samun muhalli ba.
Gwamnatin ta jaddada cewa Bala Mohammed yana cikin sahun gaba wajen kokarin farfaɗo da PDP daga rikice-rikicen da ake ƙoƙarin jefa ta ciki, kuma hakan ya tabbatar da cewa kwarewarsa ta jagoranci ba ta bukatar ƙarin tantancewa, musamman ganin nasarorin da ya samu a cikin manyan zabukan da ya kayar da PRP sau biyu.
Sanarwar ta aika da sakon gargadi ga al’ummar Bauchi musamman magoya bayan PDP da su kasance masu lura wajen kare nasarorin da aka samu a fannonin ci gaban karkara, ayyukan more rayuwa, yawon bude ido da sauran muhimman manufofi, domin kada su fada hannun masu neman amfani da siyasa wajen cutarwa.
NAN













































