Gwamnatin Kano Kano ta kammala tsarin samar da manyan magudanan ruwa domin kiyaye ambaliyar ruwa a Birane 

WhatsApp Image 2025 12 10 at 23.53.54 750x430

Gwamnatin jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf na ƙara himma wajen tsaftace muhalli, ƙarfafa juriya ga ambaliya a birane da inganta kula da ruwan sama a fadin jihar.

A wata sanarwa da kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar, Dakta Dahiru M. Hashim ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa ya kai ziyarar duba manyan ayyukan magudanan ruwa da ake gudanarwa a unguwannin Giginyu, Badawa da Ladanai a ƙaramar hukumar Nasarawa domin tantance matakin aikin da ma’aikatar ke aiwatarwa.

Sanarwar ta bayyana cewa waɗannan ayyuka da ake yi za su rage matsanancin ambaliya da ke barazana ga rayuka da dukiya da muhimman gine-gine musamman a lokacin damina, inda ake fuskantar taruwar ruwan sama mai yawa a wasu yankuna.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa kwamishinan ya kuma bayyana cewa bayan waɗannan ayyukan na musamman, gwamnatin jihar na kan aikin samar da cikakken babban tsari na magudanan ruwan jihar wanda zai kasance tubalin tsara ayyukan magudanan ruwa na gaba.

Karin labari:Adadin wadanda suka mutu a ambaliyar Niger ya kai 151, mutum fiye da 3,000 sun rasa muhalli

Ya bayyana cewa shirin zai samar da ingantaccen tsari na bayanai domin tabbatar da cewa duk ayyukan da ake yi na gine-gine da magudanan ruwa sun dace da yanayin canjin yanayi, sun bi ƙa’idar injiniya kuma sun dace da yawan faɗaɗar birane da ake fuskanta a jihar.

Dakta Hashim ya yi kira ga mazauna jihar su ɗauki nauyin haɗin guiwa wajen kare kadarorin gwamnati ta hanyar guje wa zubar da shara cikin magudanan ruwa da kuma tallafawa aikin share magudanan akai-akai domin samun gudanawar ruwan sama yadda ya kamata.

Ma’aikatar ta jaddada cewa aiwatar da waɗannan ayyukan yadda ya kamata zai rage haɗarin ambaliya, ya kare al’umma daga barna, kuma ya ƙara ƙarfafa juriya ga matsalolin muhalli da ake fuskanta a fadin jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here