Rigimar Masarauta: Gwamnan Kano ya bada umarnin kama masu yin taruka da zanga-zanga dana Dalibai

Abba Kabir Yusuf, masarauta, zanga-zanga, kano, jihar
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya takunkumi mai tsauri a kan duk wani taron jama'a da aka yi niyyar gudanar da zanga-zanga a jihar, tare...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya takunkumi mai tsauri a kan duk wani taron jama’a da aka yi niyyar gudanar da zanga-zanga a jihar, tare da yin amfani da ikon da aka ba shi a matsayin babban jami’in tsaro na jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Laraba.

Karin labari: Da Dumi-Dumi: Gwamnan Kano ya umarci jami’an tsaro su kama masu zanga-zanga

SolaceBase ta rawaito cewa tun bayan rusa masarautu guda 5 aka maido da Malam Muhammadu Sanusi II tare da tsige Alhaji Aminu Ado Bayero aka yi ta zanga-zanga a tituna da kuma fargabar karya doka da oda.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, ”Saboda mukaminsa, gwamnan ya umarci ‘yan sanda, da hukumar tsaro ta farin kaya, da ta kasa da su kama tare da tsare da kuma gurfanar da duk wani mutum ko kungiyar da ke gudanar da zanga-zangar a gaban kotu ko kan titunan Kano.

Karin labari: Kotuna guda biyu sun ba da umarni daban-daban kan korar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu

”Wannan matakin da aka dauka wani shiri ne na riga-kafi da nufin dakile duk wani abu da zai iya haifar da rugujewar doka da oda da makiya jihar suka shirya.”

“Gwamnan ya bukaci daukacin al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum domin jihar ta ci gaba da zaman lafiya, kuma gwamnati za ta ci gaba da sanya ido kan lamarin don gaggauta magance duk wani mutum ko kungiyar da ke kokarin kawo cikas ga zaman lafiyar jihar.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here