Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ba zai miƙa wa gwamnatocin jihohin kasar nan ba ragamar tafiyar da jami’o’in gwamnatin tarayya.
A Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya fitar ya ce sun lura cewa an juya maganar da ɗan takarar shugaban kasar na PDP ya yi a wajen wani babban taro na kungiyar lauyoyin Najeriya da ya gudana a Legas, a kan batun da ya shafi bangaren ilimi da hanyoyin da zai bi wajen warware matsalolin da bangaren ke fuskanta.
Ya ce a cikin bayanan Atiku, bai ce zai mika ragamar kula da jami’in gwamnatin tarayya ga jihohi ba idan har aka zabe shi a zaben shugaban kasa mai zuwa.
“Wannan ba daidai ba ne don bai fadi haka ba a lokacin da yake bayar da amsa a kan tambayoyin da aka yi masa game da manufofinsa” in ji shi.
Ya ce abin da Atiku Abubkar yake nufi shi ne matakan da zai bi daki-daki na rage wa gwamnatin tarayya nauyin tafiyar da jami’o’in da ke karkashinta.
A don haka batun cewa zai mika wa gwamnatocin jihohi ragamar tafiyar da jami’oi ba gaskiya ba ne.












































