Majalisar wakilan Tarayya zata fara gudanar da bincike Kan harin da aka Kai gidan gyaran hali na Kuje

Reps new
Reps new

Kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin tsaro da leken asiri, ya fara gudanar da bincike kan harin da aka kai a gidan yari na Kuje wanda ya kai ga tserewa fursunoni 64.

Shugaban kwamitin, Sha’aban Sharada, ya ce kudurin majalisar na binciken harin ya biyo bayan kudirin da aka gabatar a zauren majalisar.

Ya ce a watan Yuli ne majalisar ta kaddamar da wani kwamitin hadin gwiwa kan harkokin tsaron kasa sakamakon harin da aka kai domin gudanar da bincike tare da samar da shawarwarin da za su hana sake aukuwar lamarin.

Sharada ya ce kwamitin zai tabbatar da irin rawar da hukumomin tsaro da na leken asiri suka taka wajen tabarbarewar tsaro tare da samar da hanyoyin dakile sake afkuwar lamarin.

Ya yi nuni da cewa hukumomin tsaro da abin ya shafa suna da tambayoyi da yawa da za su amsa dangane da tabarbarewar tsaro da ya jawo wa gwamnatin tarayya babban abin kunya.

A cewarsa, an yi hakan ne domin a tabbatar da yanayin da aka gudanar da shi a wani yunkuri na magance dukkan kalubalen tsaron kasar nan.

Sha’aban Sharada ya kuma bukaci jami’an tsaro da su samar da bayanai masu amfani domin samun nasarar aikin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here