Rundunar sojin ta amince da karin girma ga wasu manyan hafsoshi 108 zuwa mukamin Manjo-Janar da Birgediya-Janar domin yabawa bajintar hidimar da suke yiwa kasa.
Karin girma, wanda ya kunshi manyan birgediya 35 zuwa manyan hafsoshin soja 73 da kuma Kanar 73 zuwa mukamin birgediya-janar, an amince da su ne a zaman majalisar na ranar Alhamis.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Maj.-Gen. Onyema Nwachukwu, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.