A yau Litinin ne gwamnatin jihar Kano ta soke takardar shedar gudanar da aiki na duk makarantu masu zaman kansu a fadin jihar.
Gwamnati ta bukaci duka makarantun da suke sake zuwa domin kara tantance su.
Solacebase ta bada rahoton cewa hakan na zuwa ne bayan kashe wata yarinya ‘yar shekara 5 mai suna Hanifa Abubakar da wani malamin makaranta mai zaman kanta ta Noble Kids Academy ya yi.
Kwamishinan jihar, Muhammad Sanusi Kiru ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a wani taron manema labarai.
A cewarsa, “dukkanin mu muna sane da yadda ake ci gaba da shari’ar mutuwar Hanifa domin wani wanda ake zargi mai suna Abdulmalik Tanko wanda shi ne mamallakin makarantar Noble Kids Academy ya yi mata kisan gilla, kuma bisa la’akari da abin bakin ciki da ya faru, musamman dangane da yadda aka kashe ta, gwamnatin jihar ta yanke shawarar janye satifiket na duk wasu makarantu masu zaman kansu don sake tantancewa.
Ya ce ma’aikatar ilimi za ta gindaya sharuddan sake tantance su.
Ya yi nuni da cewa, an kafa wani kwamiti da ya kunshi ma’aikatar shari’a, jami’an tsaro na DSS da Civil Defence da sauran hukumomin da za su duba batun sabunta rijistar makarantu masu zaman kansu a jihar Kano.













































