Rundunar ‘yan sanda a ranar Litinin ta gurfanar da Abdulmalik Tanko, wanda ya kashe Hanifa Abubakar ‘yar shekara 5.
Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Abdulmalik Tanko, Hashim Issyaku da Fatima a gaban Alkalin Kotun Mai shari’a Muhammad Jibir, dake Gidan Murtala, babban birnin Kano, bisa tuhumar su da laifin hada baki, Satar yarinya, boye ta tare da kasha ta.
Solacebase ta ruwaito cewa an sace Hanifa Abubakar ne a ranar 4 ga watan Disamba 2021 a kan hanyarta ta dawowa daga Islamiyya da malaminta, daga bisani kuma aka kashe ta bayan an biya miliyan 6 kudin fansa.
A makon da ya gabata ne ‘yan sanda suka kama wanda ya yi kisan da kuma wadanda suka hada baki.
Ba a wakilce wadanda ake tuhumar yayin da Barr. Lamido Soron Dinki shi ne Lauyan da ya shigar da kara.
Bayan an karanta wa wadanda ake tuhumar laifin an tsare su a gidan yari, inda za’a ci gaba da shari’ar a ranar 2 ga Fabrairu, 2022.













































