
‘Yan kasuwar Singa a Kano sun musanta zargin da ake musu na boye kayayyakin masarufi domin daga farashinsu, ‘yan kasuwar sun dauki wannan mataki ne bayan da Hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta PCACC tayi musu dirar mikiya inda ta barke wasu manyan rumbuna da tarin kayayyakin abinci.
‘Yan kasuwar sun wanke kansu daga zargin da ake musu na boye kayayyakin masarufi domin safararsu zuwa kasashen dake makobtaka da Najeriya.
Karanta wannan: “Za mu nemi Naira Miliyan 1 a matsayin mafi karancin albashi” – NLC
Sun kuma kai ziyara ofishin hukumar PCACC domin cire kansu daga zargi, yayin da suka sha alwashin ci gaba da sayar da hajojinsu akan farashin da aka sani.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Ibrahim Danyaro ya yi wannan jawabi ne bayan ganawar da suka yi da hukumar ta PCACC.
A ranar Lahadin da ta gabata ne hukumar ta kai sumame wasu shaguna da ake zargin an cike su makil da kayayyaki tare da rufe su domin boyewa saboda farashin kayan ya tashi.