Da Dumi-dumi: Akpabio ya rantsar da sabbin Sanatoci 3

Majalisar, Dattawa, sanatoci, rantsar
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya jagoranci rantsar da sabbin zababbun Sanatoci 3 a zaman da aka yi ranar Talata. ‘Yan majalisar su ne...

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya jagoranci rantsar da sabbin zababbun Sanatoci 3 a zaman da aka yi ranar Talata.

‘Yan majalisar su ne Prince Pam Mwadkon na ADP daga Plateau North da Farfesa Anthony Ani na APC daga Ebonyi South sai kuma Mustapha Musa na APC daga Yobe ta Gabas.

Karanta wannan: ‘Yan kasuwa a Jihar Kano sun musanta zargin boye kayan abinci

Magatakardar majalisar dattawa Mista Chinedu Akubueze ne ya gudanar da rantsuwar da misalin karfe 11:41 na safe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here