Tinubu ya sauya sunan Cibiyar Man Fetur ta Kaduna zuwa sunan Shehu Yar’Adua

images 51

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Cibiyar Nazarin Man Fetur dake Kaduna, zuwa Jami’ar Kimiyyar Geoloji da Fasahar Injiniya ta Janar Shehu Musa Yar’Adua.

Tinubu ya sanar da wannan matakin ne a ranar Juma’a a yayin jawabinsa na murnar Ranar Dimokuradiyya ta wannan shekara.

Shugaban ya bayyana Yar’Adua a matsayin daya daga cikin mutanen da suka taimaka wajen tsara dimokuradiyyar Najeriya ta wannan lokacin.

“Kowace zamani da al-umma tana da aikin da ya ratayu a kanta. Magabatanmu sun tabbatar da samarwa kasar nan ‘yancin kai, al-ummar 12 ga Yuni sun tabbatar da dimokuradiyya. Mu kuma dole ne mu tabbatar da wadata,” in ji shi.

“Mu hada kai tare, mu manta da rarrabuwa, rashin bege, da tsananin rai; mu rungumi hadin kai, bege, da kwarin gwiwa, mu gina Najeriya da zata hadu kan manufa guda, wadda bambancin ta ya karfafa ta, inda adalci zai samu samu, ‘yanci ya tsira, da damamarmaki su wadata.

“Daga cikin mutanen da suka tsara dimokuradiyyar Najeriya ta zamani, mun karrama Janar Shehu Musa Yar’Adua saboda hangen nesan sa na hadin kan kasa.

“Don karrama gudummawarsa, gwamnatin tarayya ta amince da sake farfado da Cibiyar Nazarin Man Fetur ta Kaduna da kuma sauya sunan ta zuwa Jami’ar Kimiyyar Geoloji da Fasahar Injiniya ta Janar Shehu Musa Yar’Adua.”

Yar’Adua fitaccen jami’in sojin Najeriya ne wanda ya yi aiki a matsayin Babban Hafsa na Ma’aikata na Hedikwatar Koli, mataimakin shugaban kasa a tsakanin 1976 zuwa 1979 a karkashin Olusegun Obasanjo, wanda shine shugaban kasa a lokacin.

Ya taka muhimmiyar rawa wajen kula da sauyin mulki na farko na Najeriya daga mulkin soja zuwa gwamnatin farar hula da aka zaba.

Bayan ya yi ritaya daga sojoji, Yar’Adua ya kafa jam’iyyar PDM, wadda ta zama mai karfi a fagen siyasar Najeriya.

Ya kasance mai suka ga mulkin soja na Sani Abacha, aka kama shi bisa zargin aikata laifin cin amanar kasa, ya mutu a gidan yari a 1997 cikin yanayi mai cike da cece-kuce.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here