Yajin aikin ASUU: Jami’ar Kaduna ta umurci ɗalibai da malamai su koma makaranta ranar 9 ga Mayu

Kaduna state university
Kaduna state university

Jami’ar jihar Kaduna KASU, ta shirya komawa harkokin karatu na kakar karatu ta 2020 zuwa 2021 a ranar 9 ga watan gobe na Mayu duk da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ASUU ke tsaka da yi na tsawon makonni goma.

A wata sanarwa da jami’ar ta fitar mai ɗauke da kwanan watan 26 ga Afrilu wadda kuma magatakardan jami’ar Abdullahi Zubairu, ya sanya wa hannu, sanarwar ta umurci ɗaukacin ɗalibai da malaman jami’ar da su koma domin ci gaba da harkokin ilimi.

Sanarwar ta kuma shawarci dukkan malamai da dalibai da su kiyaye wajen yin aiki da kalandar zangon karatun kamar yadda take.

Yajin aikin ƙungiyar dai ya tsawaita zuwa watanni biyu wanda har kawo yanzu ba a cimma daidaito ba tsakanin malaman da gwamnatin tarayya biyo bayan gaza biya musu buƙatun da suka gabatar.

Cikin damuwa da halin da ake ciki, daliban Najeriya da dama sun shiga shafukan sada zumunta suna nuna rashin amincewarsu dakatar da harkokin karatun.

A makon da ya gabata ne ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya ce, matakin dakatar da yajin aikin da ƙungiyar ta ASUU ta ɗauka, ƙungiyar ce kaɗai za ta iya magance shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here