An rantsar da Soludo a matsayin gwamnan Anambra 

Charles Soludo
Charles Soludo

An rantsar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Farfesa Charles Chukwuma Soludo a matsayin gwamnan farar hula na biyar a jihar Anambra.

Farfesa Soludo, wanda ya lashe zaben gwamna a ranar 9 ga watan Nuwamba, 2022 a karkashin jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), an rantsar da shi ne a yau Alhamis a wani biki da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Awka, babban birnin jihar.

Ya karbi mulki daga hannun Willie Obiano wanda wa’adinsa na shekaru takwas ya kare a yau, Alhamis.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here