Yanzu-yanzu: Majalisar dokokin Kano ta tantance Mustapha Kwankwaso

Mustapha, Rabi'u, Kwankwaso, majalisar, dokokin, kano, tantance, kwamishina
A ranar Talata ne Majalisar dokokin jihar Kano ta tantance Mustapha Rabi'u Kwankwaso a matsayin kwamishina. Tunda fari dai, Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba...
A ranar Talata ne Majalisar dokokin jihar Kano ta tantance Mustapha Rabi’u Kwankwaso a matsayin kwamishina.
Tunda fari dai, Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya aike da sunan Mustapha Rabiu Kwankwaso, wanda dane ga tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso da wasu mutane uku zuwa majalisar dokokin jihar domin tantance su a matsayin kwamishinoni.

Karin labari: Gwamna Yusuf Ya Nada Dan Kwankwaso Da Wasu Mutane 3 A Matsayin Kwamishinoni

Idan ba’a manta ba, jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa a wata takarda da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aikewa shugaban majalisar dokokin jihar Kano ya bukaci majalisar ta amince da nada Adamu Aliyu Kibiya da Abduljabbar Umar Garko da Shehu Sule Aliyu Karaye da kuma Mustapha Rabiu Kwankwaso a matsayin kwamishinoni.

Karin labari: Shugabar mata a jam’iyyar NNPP ta yi murabus

Wanda majalisar ta cika alkawarinta na tantance su a ranar Talata 2 ga watan Afrilun, 2024.

A baya dai an ta samun cece-kuce kan nada Mustapha a matsayin kwamishina bisa ganin cancantarsa ko akasin haka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here