Aƙalla mutum 27 aka kashe, ɗaya kuma na cikin mawuyacin hali sakamakon wata gobara da ta tashi a wani gidan rawa a Turkiyya.
An rufe gidan rawar da ke ƙarƙashin wani dogon gini a Instanbul, kuma ana gyare-gyare.
Da yake magana da kafafen yaɗa labarai, gwamnan Instanbul Davut Gül ya ce ba’a gano abin da ya janyo tashin gobarar ba.
Karin labari: Yanzu-yanzu: Majalisar dokokin Kano ta tantance Mustapha Kwankwaso
Ya ƙara da cewa jami’an hukumar kashe gobara na gudanar da bincike.
Magajin garin Instanbul, Ekrem Imamoglu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan da lamarin ya shafa.