Ministan tsaro ya kai ziyara ga iyalin marigayi Janar Uba

XGltYWdlc1xjb250ZW50XDEyMTEyMDI1MTAzNzE5X2c3NmFybWd3b2FldXVtczEuanBnfDY3MHwxMi8xMi8yMDI1 670x430

Ministan tsaro janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya ya sami yabo kan ziyarar ta’aziyya da ya kai wa iyalin marigayi Birigediya Janar B. M. Uba wanda ya rasu yayin aikin yaki da Kungiyar Boko Haram da Kungiyar ISWAP a wani samame da aka yi a Wajiroko a ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Wata sanarwa daga Edward John Auta Pama wanda masani ne kan tarihi da al’amuran jama’a kuma mai fafutukar ganin an gina ingantacciyar gwamnati ya bayyana cewa ministan ya kai wannan ziyara a ranar Alhamis domin jajanta wa iyalan tare da tabbatar da goyon bayan gwamnatin tarayya da al’umma gaba ɗaya.

Sanarwar ta nuna cewa zuwan Janar Musa ya ba da kwarin gwiwa da ta’aziyya ga iyalan, lamarin da ya zama sakon godiya ga sadaukarwa da marigayin ya yi wajen kare ƙasa da ‘yan kasa.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa irin wannan halayya ta nuna tausayawa da jagoranci mai inganci ita ce ta bambanta lokacin da ya jagoranci rundunar tsaro a matsayin babban hafsan tsaro wanda hakan ya inganta matsayin sa na jajirtaccen shugaba.

A cewarsa ‘yan Najeriya na da kwarin gwiwa cewa nadin janar Musa zai ƙara wa bangaren tsaro kuzari da tsari da kuma manyan nasarori a fannin kare ƙasa.

Ya ƙara da cewa irin ayyukan girmama jaruman da suka sadaukar da rayukansu na daga abin da ke ƙara ɗaga ƙwarin gwiwar jami’an tsaro da ke ci gaba da kare al’umma tare da fatan alkhairi ga Janar Musa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here