Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bawa gwamnatin Najeriya hakuri, Maniyata da kuma sauran duk wadan da suka fatawa, sakamakon gazawar su na kai alhazain Najeriya 1,550 kasar Saudiya don gudanar da aikin Hajjin bana.
Bayanin hakan na dauke cikin wata sanarwa da mataimakiyar darakta na hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar yau Juma’a.
Tace hukumar NAHCON ta yi dana sanin abinda ya faru da alhazan Najeriya, na wahalhalu da bacin rai da suka fuskanta, dama gaza kai wasu aikin hajji.













































