Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bukaci a saki ko kuma a gurfanar da malamin addini da ke Kaduna, Sheikh Sani Khalifa Zaria nan take, bisa tsare shi na tsawon lokaci ba tare da an kai shi gaban kotu ba.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba daga ofishin yada labaransa, Atiku ya bayyana cewa ci gaba da tsare malamin tun daga watan Disamba na shekarar 2025 na karya hakkin dan Adam na asali.
Sanarwar da mataimakinsa Paul Ibe ya wallafa a shafin X ta nuna cewa ana tsare da Sheikh Khalifa ne bisa zargin alaka da yunkurin juyin mulki, amma har yanzu ba a gurfanar da shi a gaban wata kotu ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya nuna damuwa cewa wannan lamari yana tayar da manyan tambayoyi kan kundin tsarin mulki da hakkin dan Adam, musamman ganin cewa akwai umarnin da wata babbar kotu ta tarayya ta bayar na a gurfanar da malamin a gaban kotu, amma ba a bi umarnin ba.
Ya kara da cewa tsare malamin ba tare da samun damar ganawa da iyalansa, lauyoyi ko samun kulawar lafiya yadda ya kamata ba na nuna take hakkin dan Adam, wanda ka iya raunana tsarin dimokuradiyya da rage mutuncin ‘yancin jama’a.
Haka kuma ya bayyana cewa jama’a na kara nuna damuwa kan halin da malamin yake ciki, inda rashin cikakken bayani daga hukumomi ke kara jawo rashin yarda da kuma rudani a tsakanin al’umma.
Atiku ya bukaci hukumomin tsaro su saki Sheikh Sani Khalifa nan take ko kuma su kai shi gaban kotu mai iko ba tare da bata lokaci ba, yana mai cewa duk wani abu sabanin haka na nuni da tsare mutum ba bisa ka’ida ba da kuma amfani da iko ba daidai ba.













































