Tinubu ya dawo Abuja bayan bikin sallah karama a Lagos

Tinubu arrival (1)

Shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba ya bar Lagos zuwa Abuja bayan kammala bukukuwan sallah karama.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya nuna cewa jirgin shugaban kasa ya tashi daga bangaren shugaban kasa na filin jirgin sama na Murtala Muhammed da misalin karfe 6:44 na yamma.

Manyan jami’an gwamnati sun raka shi zuwa filin jirgin, ciki har da gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu, mataimakinsa Obafemi Hamzat da manyan jiga-jigan APC.

A lokacin zamansa a Lagos, Tinubu ya halarci sallar idi a Dodan Barracks tare da karbar bakuncin wasu shugabannin siyasa da na tattalin arziki.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas.

Haka kuma wasu gwamnonin jihohi da manyan ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na kasar nan sun halarci tarukan.

Shugabannin bangaren masu zaman kansu ciki har da Aliko Dangote sun halarci wadannan ganawa, tare da wakilan kasashen waje ciki har da tawaga daga Tarayyar Turai.

An bayyana cewa wadannan ganawa na daga cikin kokarin karfafa hadin kan kasa da kuma inganta hadin gwiwa tsakanin bangarorin siyasa da tattalin arziki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here