Gwamnatin tarayya ta ce ta dakatar da shirin N-Power har sai baba ta gani.
Ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu, ta sanar da dakatarwar ne a ranar Asabar a wata hira da ta yi da gidan talabijin na TVC News.
A cewar Edu, an yanke hukuncin ne saboda wasu kura-kurai da aka samu a cikin shirin. A halin da ake ciki, ministan ta ce gwamnati ta fara gudanar da bincike kan yadda aka yi amfani da kudaden tun da aka fara shirin.
Ta bayyana cewa ba a samun wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin a wuraren da aka tura su aiki duk da haka suna tsammanin biyan alawus na wata-wata.
Ministan ta ce ya kamata wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin su fice daga shirin tun 2022 amma har yanzu suna kan biyan albashi.