Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa da ya gabata, Atiku Abubakar ya bayyana cewa yakin da ya ke yi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana da amfani ga al’ummar Najeriya baki daya.
Ya fadi hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja, ya ce yakin da ake yi da cancantar Tinubu a matsayin shugaban kasa na da manufar kafa shugabanci nagari, da rikon amana, da kuma sahihanci a aikin gwamnati.
Atiku wanda ya samu rakiyar wasu tsofaffin gwamnonin jihohi da jiga-jigan jam’iyyar PDP a wajen taron, ya sha alwashin cigaba da yakar Tinubu.