Hukumar NRC ta bayyana lokacin da jirgin kasan Kaduna zuwa Kano zai fara aiki

Hukumar, NRC, bayyana, lokacin, jirgin, kasan, Kaduna, Kano, fara, aiki
Jirgin kasan Kaduna zuwa Kano zai fara aiki ne a farkon kwata na farko na shekarar 2025, kamar yadda Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa (MD/CEO)...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Jirgin kasan Kaduna zuwa Kano zai fara aiki ne a farkon kwata na farko na shekarar 2025, kamar yadda Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa (MD/CEO) na Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC), Mista Fidet Okhiria ya bayyana.

Okhiria ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci tashar jirgin kasa ta Rigasa da ke Kaduna sakamakon barnar da aka samu a hanyar.

Sai dai ya koka da tsadar man dizal da rashin tsaro, wanda a cewarsa yana kawo tsaiko a harkokinsu da ayyukan jiragen kasa.

Karin labari: “Nan ba da jimawa ba za’a aika da kudirin dokar sabon mafi karancin albashin ma’aikata” – Tinubu

Da yake magana yayin gabatar da tambayoyi daga manema labarai, Manajan Daraktan ya ce, “Lokacin da muka fara, tallafin ya yi yawa amma bayan harin da aka kai a watan Maris 2023, abubuwa sun lalace.

“Muna tafiyar da jiragen kasa guda 10 a lokacin amma bayan faruwar lamarin da ma saboda tsadar man dizal, sai da muka kayyade adadin lokutan kuma mun rage ayyukanmu zuwa hasken rana kawai.

“A lokacin da muka fara, man dizal yana tsakanin Naira 230 zuwa Naira 280 a kowace lita, yanzu farashinsa tsakanin Naira Dubu 1,000 zuwa Naira Dubu 2,000 ya danganta da mai kawo kaya kuma saboda layin dogo na jama’a ne, gwamnati ta yanke shawarar kula da farashin domin mutane su samu jindadin abin da gwamnati ke bayarwa.”

Karin labari: Majalisar wakilan Najeriya ta nada sabbin shugabannin kwamitoci

Ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa nan gaba kadan kamfanin zai tura fasahar sa ido kan jirgin kasa da hanyoyin mota kamar wayar hannu domin magance barna a fadin kasar nan.

Okhiria ya kara da cewa ya lura tun lokacin da aka bullo da tikitin an rage yawan barace-barace zuwa mafi karanci.

“Mun yi ƙoƙarin iyakance hulɗar ma’aikata tare da abokan ciniki ta hanyar tabbatar da cewa sun sayi tikitin kan layi kuma akwai kayan aikin da ke duba abokan ciniki a ciki da waje,” in ji Manajan Daraktan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here