“Nan ba da jimawa ba za’a aika da kudirin dokar sabon mafi karancin albashin ma’aikata” – Tinubu

Shugaba, Tinubu, faɗuwa, rusuna, girmama, dimokuraɗiyya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya mayar da martani kan faduwar da ya yi lokacin bikin ranar dimokuraɗiyya ta 12 ga watan Yunin 2024...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu, ya baiwa kungiyar kwadago tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a aika da wani kudirin doka kan sabon mafi karancin albashi na ma’aikata na kasa zuwa majalisar dokokin kasar domin amincewa da shi.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a jawabinsa na ranar Dimokuradiyya na biyu a ranar 12 ga watan Yunin 2024.

Karin labari: Majalisar wakilan Najeriya ta nada sabbin shugabannin kwamitoci

“A cikin wannan batu, mun yi shawarwari cikin aminci kuma da hannu biyu-biyu tare da Kungiyoyin Kwadago kan sabon mafi karancin albashi na kasa.

“Nan ba da jimawa ba za mu aika da wani kudurin doka na zartarwa ga Majalisar Dokoki ta kasa don sanya abin da aka amince da shi a matsayin wani bangare na dokar mu na tsawon shekaru biyar ko kasa da haka,” in ji Shugaban.

Cikakken labarin na tafe…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here