Majalisar wakilan Najeriya ta nada sabbin shugabannin kwamitoci

Majalisar, wakilan, Najeriya, nada, sabbin, shugabannin, kwamitoci
Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, ya yi ‘yan sauye-sauye a shugabancin wasu kwamitocin majalisar, domin karfafa sa ido da tabbatar da inganci...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, ya yi ‘yan sauye-sauye a shugabancin wasu kwamitocin majalisar, domin karfafa sa ido da tabbatar da inganci.

Abbas ya sanar da sabbin shugabannin yayin zaman majalisa a Abuja ranar Talata.

Ya ce, Dan Majalisa Abdulmumin Jibrin na jam’iyyar NNPP, a jihar Kano shi ne sabon shugaban kwamitin gidaje da muhalli na majalisar.

Karin labari: Zan Aike Wa Majalisa Ƙudiri Game Da Sabon Mafi Ƙarancin Albashi — Tinubu

Sauran sabbin shugabannin sun hada da Oluwole Oke na jam’iyyar PDP, a jihar Osun matsayin shugaban harkokin kasashen waje, sai Aminu Balele na jam’iyyar APC, a jihar Katsina, da Dan majalisa Mamudu Abdullahi na jam’iyyar APC, na jihar Niger a matsayin Ma’aikatar shari’a.

Jibrin wanda ya kasance dan majalisar a karo na hudu, ya taba rike mukamin shugaban kwamitocin kudi da kasafin kudi da na sufuri da harkokin kasashen waje.

Karin labari: Tinubu zai yi wa ƴan Najeriya jawabi a safiyar Laraba

NAN ta rawaito cewa, a bangaren zartarwa, Jibrin ya kuma taba zama Babban Darakta na Hukumar Kula da Gidaje ta Tarayya (FHA).

Shugaban majalisar ya ce, kulawa da hurumin kwamitin majalisar kan gidaje da muhalli ya shafi ma’aikatar gidaje ta tarayya da ma’aikatu da hukumominta.

A baya Oke ya jagoranci kwamitocin majalisar kan harkokin kudi da shari’a, yayin da Abdullahi da Balele suka jagoranci kwamitocin majalisar kan sojoji da gidaje.

Karin labari: Rikicin Masarautar Kano: Alhaji Aminu Ado Bayero ya umarci Hakimai su shirya hawan Sallah Babba

Majalisar ta kuma bayyana kundin tsarin mulkin wani kwamitin wucin gadi da zai binciki yadda aka rufe wasu kasuwanni a kasar.

Kwamitin zai binciki ficewar Messrs Kimberly-Clark da wasu kayayyaki na kasuwanci daga kasar, wanda dan majalisa Kayode Akiolu na jam’iyyar APC a Legas da zai jagoranta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here