
Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
A ranar Talata ne sanarwar Alhaji Aminu Ado Bayero, daga masarautar Kano ta bayyana inda ya umarci Hakimai da Dagatai da su shigo cikin jihar don fara shirye-shiryen hawan sallah babba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 10 ga watan June, 2024 da Galadiman Kano Alhaji Abba Sunusi ya rattabawa hannu.
Karin labari: Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a Katsina
Sanarwar ta kuma bukaci Hakiman da su shigo cikin Kano da Dagatansu, mahaya da kuma dawakansu, domin shirye-shiryen fara hawan sallah babba.
Idan dai ba’a manta ba a makonnin da suka gabata, SolacBase ta rawaito cewa dambarwar masarautar Kano ta samo asali ne tun bayan da gwamnatin Kano ta tsige Alhaji Aminu Ado Bayero daga masarautar tare da maye gurbin shi da Muhammadu Sanusi II.