Hukumar EFCC ta kama ‘yar kasuwar nan Aisha Achimugu da ake nema ruwa a jallo a filin jirgin sama na Abuja

Aisha Achimugu and EFCC 750x430

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta cafke fitacciyar ‘yar kasuwa, Aisha Sulaiman Achimugu, a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

A cewar wata sanarwa daga lauyanta, Cif Chikaosolu Ojukwa ya fitar a ranar Talata, ya ce an kama Achimugu da misalin karfe 5 na safe a lokacin da ta iso daga Landan.

Kamen dai na da nasaba da binciken da hukumar EFCC ke yi na hada baki da kuma karkatar da kudade.

Tun da farko lauyanta ya sanar da babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa Achimugu ta bayyana aniyar ta, ta hanyar takardun kotu, don girmama gayyatar da EFCC ta yi mata a ranar Talata.

Karanta: Gwamna Bala ya naɗa mataimakan siyasa 168

Hakan ya biyo bayan umarnin kotu da mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar, inda ya umurci Achimugu ta girmama gayyatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa a ranar 29 ga Afrilu, 2025.

Kotun ta kuma ba da umarnin ta bayyana a gaban ta ranar Laraba, 30 ga Afrilu, 2025, don ci gaba da shari’a kan lamarin.

Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, bai amsa kira ko sako ba har zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here