Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja ta samu nasarar kwato wasu motoci guda uku da aka sace tare da cafke wasu mutane takwas da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da miji da mata da suka yi amfani da kayan aikin da aka siya ta internet wajen aikata laifukan.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Josephine Adeh ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
A cewar sanarwar, an fara aikin ne a ranar 19 ga Afrilu, 2025, bayan da aka samu rahoton sace wata mota kirar Toyota Corolla (mai lamba ABC 570 FJ) daga sakatariyar gwamnatin tarayya.
Jami’an rundunar ‘yan sanda ta Scorpion Squad sun kama wani Yusuf Yunusa da laifin satar, kuma suka ci gaba da bincike wanda ya kai ga cafke matarsa, Blessing Yusuf, a karamar hukumar Kwali a ranar 25 ga Afrilu.
“Lokacin da ake yi mata tambayoyi, Blessing ta amsa cewa ta sayi makullan Toyota masters daga kasuwar Jumia ta internet, wanda mijin nata ya rika satar ababen hawa”.
A wani lamari na daban, a ranar 28 ga Afrilu, ‘yan sanda sun samu wani rahoto daga wani mai siyar da mota a Life Camp game da batan wata baƙar mota Mercedes-Benz 4MATIC E-400 (lambar rajista AAA 07 KA).
Karin karatu: Hukumar EFCC ta kama ‘yar kasuwar nan Aisha Achimugu da ake nema ruwa a jallo a filin jirgin sama na Abuja
Bincike ya tabbatar da cewa an sace motar ne daga Lekki da ke Legas, sai dai sn kama mutane biyar da ake zargi – Idris Suleiman, Isiyaku Habibu, Ganiyu Sadiq, Idowu Akintunde, da Bello Muyideen. An gano cewa wadanda ake zargin sun sace motar ne daga hannun mai aikinsu.
Tuni dai aka gano motar.
Hakazalika, jami’an sashin Mabushi sun kaddamar da wani samame ne biyo bayan korafin da Chinwenze Chinaza ya yi, inda ya bayyana cewa direbansa mai suna George Idung ya bace tare da wata mota kirar Toyota Hilux Adventure da ba a yi mata rajista ba. Bisa ga sahihan bayanan sirri, ‘yan sandan sun bi sawun Idung zuwa garinsu da ke karamar hukumar Eket a jihar Akwa Ibom, inda aka kama shi a lokacin da yake kokarin sayar da motar, kuma aka kwato motar.
A halin yanzu dai dukkan mutanen takwas suna tsare kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.
“Kwamishanan ‘yan sanda reshen babban birnin tarayya Abuja, CP Ajao S. Adewale, ya bukaci mazauna yankin da su sanya na’urorin bin diddigi a cikin motocinsu, su guji ajiye motoci a wurare da babu jama’a, sannan su tabbatar da mallakar motocin kafin su saya,” in ji sanarwar.