Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar ma’aikata ta bana, wadda ake gudanarwa duk shekara a ranar 1 ga watan Mayu.
Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida ne ya sanar da hutun a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Tunji-Ojo ya yabawa ma’aikatan Najeriya bisa jajircewa da sadaukarwar da suka yi, tare da la’akari da kokarin da suke yi a matsayin masu bayar da gudunmawa ga ci gaban kasa.
Ya nanata bukatar samar da zaman lafiya domin bunkasa masana’antu da bunkasar tattalin arziki sannan ya bukaci ma’aikata da su yi koyi da al’adun kirkire-kirkire da samar da albarkatu.
Ministan ya kuma karfafa gwiwar ma’aikata da su kara kaimi wajen bunkasa sana’arsu, inda ya bayyana cewa hakan zai inganta harkokin mulki tare da baiwa ‘yan kasa damar cin gajiyar dukiyar kasa.













































