Yanzu-yanzu: Ba za mu iya kwaso dalibanmu a Sudan yanzu ba – Gwamnatin tarayya.

Gwamnatin Tarayya ta ce kwaso dalibai ‘yan Najeriya a Sudan ba zai yiwu ba a halin yanzu.

‘Yan Najeriya da suka makale a rikicin da ake fama da shi a Sudan sun yi ta rokon hukumomim Najeriya dasu kwashe su.

Idan dai za a iya tunawa, fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun janar-janar guda biyu bai nuna alamun tsagaita wuta ba gabanin bukukuwan karshen watan Ramadan.

Sama da mutane 300 ne aka kashe tun bayan barkewar fadan a ranar Asabar tsakanin dakarun da ke biyayya ga Hafsan Sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa, Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar runduna ta Rapid Support Forces (RSF).

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Uwargida Abike Dabiri-Erewa ta ce yayin da tawagar Najeriya da ke Sudan da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (NEMA), suka tsara shirin kwashe daliban Najeriya da sauran ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan, yanayin tashin hankali ya sa ya zama mai matukar hadari kuma ba zai yiwu ba ga kowane jirgin sama a wannan lokaci.

Sanarwar wacce take dauke da sa hannun Gabriel Odu na sashin yada labarai, hulda da jama’a ta rawaito Dabiri-Erewa na cewa an kona jiragen da suka faka a filin jirgin saman kasar a safiyar ranar Juma’a.

Ta ce kungiyoyin agaji na neman hanyoyin samun abinci, ruwa da magunguna ga mutane.

“Saboda haka ta yi kira ga bangarorin da ke fada da juna da su yi la’akari da yarjejeniyar zaman lafiya ta Juba da kungiyar raya kasashe ta IGAD ta ayyana a matsayin wani muhimmin tsari na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here