A cikin darennan kimanin matasa guda biyar ne aka tabbatar sun mutu ayayin dasuke kokarin tsallaka kogi cikin kwale kwale.
Rahotanni sun ce samarin masu jini a jika na kokarin haurawa zuwa uzurin su bayan hawa jirgin kwale kwale a Hausawa kanwa dake bakin kogi.
“A kan ido na suka hau kwale kwalen domin kai su mahaya dazasu dauki hanya zuwa sha’anonin su na rayuwa domin kaga yanzu lokaci ne na gudanar da bukukuwan sallah” Acewar shaidar gani da ido
Matukin kwale kwalen bayan fara tafiya acikin ruwa rahotanni suka ce ya fara jin wata juwa na diban sa, inda nan take sitiyarin sandar tuka kwale kwalen tayi masa nauyi, inda duk kokarin sa na daudaita al’wmuran abun yaci tura.
Da fari kwale kwalen ya fara tangal tangal adaidai lokacin da igiyoyin ruwa ke cigaba jujjuyawa lamarin da ya sanya kifewar jirgin kwale kwalen.
Masu aikin ceto tuni sukayi nasarar tsamo gawarwakin samarin guda 5 wanda izuwa yanzu shugabannin suke ajiye da gawarwakin kafin daga bisani a gano iyalai da ‘yan uwan masu gawar.
Muna tafe da cikakken rahoto gaba kadan.
Alokacin tattara wannan rahoto












































