Kamfanin shirya gasar cin kofin kwararru ta kasa LMC ya maida Kano Pillars ta ci gaba da buga wasanninta a filin wasa na MKO Abiola dake Abuja.
“Daga yanzu Kano Pillars “Sai Masu Gida” zasu ci gaba da buga wasanin su ne da suka rage na gasar cin Kofin kwararru na Kasa ta Kakar wasannin 2022/2022 a Abuja”.
Wannan mataki ya biyo bayan hargitsi da magoya bayan kungiyar suka tayar yayin wasansu da Kungiyar Katsina United a wasan mako na 23 da ya gudana ranar Asabar, a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a Kano, lamarin da ya kai ga farfasa motar Yan wasan Katsina United.
A cikin wata sanarwa da Kamfanin na LMC ya fitar a ranar Lahadi, ya ci tarar Kungiyar ta Kano Pillars har Naira Miliyan 9, bisa karya dokokin Hukumar kwallon kafa ta kasa NPFL.
Haka kuma sanarwar tace za a zabtare maki Uku daga Kungiyar ta Kano Pillars daga cikin makin da ta samu a wannan kakar wasannin.
Kazalika Kamfanin na LMC ya kuma sake dauke Kano Pillars da ci gaba da buga wasanni a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano, har sai abinda hali ya yi.
Haka kuma Kamfanin na LMC ya kuma umarci Kungiyar ta Pillars dasu gyarawa Yan wasan Katsina United motar su ko kuma su sayo musu wata.
Wasan dai na ranar Asabar din an kammala shi a mintuna na 82 da fara wasa kunnen Doki 0-0 kowa na nema.
Yanzu haka dai Kano Pillars ta 13 da maki 27 a saman teburin Gasar ta cin kofin kwararru ta Najeriya.













































